Siyasa na haddasa rikicin addini a Nigeria

Hakkin mallakar hoto kukahfacebook
Image caption Bishop Mathew Hassan Kukah

A Najeriya, wasu masana da kuma masu son a zauna lafiya tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista a kasar, sun gudanar da taro a Abuja domin lalubo hanyoyin kyautata dangantaka tsakanin mabiya addinan biyu.

Masana daga kasashe daban-daban ne suka halarci taron na hadin gwiwa ne tsakanin cibiyar Kukah Centre da kuma cibiyar Katolika da ke Amurka.

Farfesa Abdullahi Ashafa, malami a jami'ar jihar Kaduna ya ce siyasa na daya daga cikin abubuwan da ke bata zama tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya da wasu kasashen Afirka.

Ya ce saboda son zuciya, wasu mutane idan sun fadi zabe, sai su dora hakan a kan bambancin addini, daga nan kuma sai fitina ta tashi.

Bishop Mathew Hassan Kukah ya ce talauci da rashin wasu abubuwan more rayuwa, kamar lantarki, da rashin aikin yi, da kuma zamba, su suka fi janyo rikici da ake dangantawa da addini.