Shi'a: JNI da CAN sun yi tsokaci

Manyan kungiyoyin addinai a Nigeria sun bukaci a gudanar da bincike kan lamarin da ya faru tsakanin 'yan Shi'a da sojoji a Zariya.

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta yi kira ga hukumomi a Najeriya da su bincika musabbain kashe-kashen da aka yi, don hana rikidewar rikicin zauwa wani abu dabam.

CAN ta nemi a koyi darasi daga rikicin Boko Haram.

Ita ma kungiyar Jama'atul Nasrul Islam ta bukaci gwamnati ta kafa kwamitin bincike domin gano abin da ya janyo mutuwar mutane a rikici tsakanin 'yan Shi'a da sojojin Nigeria.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga rahoton Nurah Muhammad Ringim daga Kaduna

Majalissun dokokin Nigeria su ma sun kafa kwamitin domin binciken lamarin.

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce bai kamata kungiyoyin addini su rika keta dokokin kasa ba, yana mai karawa da cewa bai kuma kamata hukumomi su yi amfani da karfin da ya wuce kima kan 'yan kasar ba.

Tuni shugaban Iran, Hassan Rouhani ya kira shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ta wayar tarho domin nuna korafinsa a kan kashe 'yan Shi'a da sojoji suka yi.