Yara 16m aka haifa ana yaki — UNICEF

Image caption Yara a duniya na ciki mummunan halin rayuwa inji UNICEF

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce yara miliyan 16 aka haifa a yankunan da ke fama da yake-yake a cikin wannan shekara.

A cewar shugaban Unicef, Anthony Lake, a ko wadanne dakikoki biyu ana haifar jariri a wurin da ake tsaka da fadace-fadace kuma yara da yawa na girma a cikin matsanancin yanayi na rayuwa - kama daga tashe-tashen hakula da bala'oi da fatara da cututtuka da kuma matsananciyar yunwa.

Wadannan alkaluma sun yi daidai da yaro daya a cikin ko wadanne yara takwas da ake haifa.

Hukumar ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar wadannan yara su mutu kafin su cika shekara biyar, sannan wadanda suka rayu za su iya samun matsala a tunaninsu.