Kotu a Brazil ta janye dakatarwar da aka yi wa WhatApp

Wani alkalin kotu a kasar Brazil ya bada umurnin janye dakartarwa da aka yi wa kamfanin sada zumunta na WhatApp.

Alkali Xavier de Souza ya umurci hukomomin kasar a kan su dawo da shafin ba tare da bata lokaci ba .

Tun farko wata kotu ta bayar da umurnin dakatar da shafin har na tsawon sa'oi 48 a ranar Alhamis bayan da kamfanin WhatApp din ya kasa yin bayani kan umurnin da wata kotu ta bayar a kan ya samar wa masu bincike da bayyannai kan wasu da ake zargi da aikata ba dai dai ba.

Sai dai alkali Souza ya ce ba dai dai bane a takurawa miliyoyin masu amfani da shafin da ke kasar.

Yan kasar Brazil sun dinga korafi a shafukan sada zumunta game da dakatarwar da aka yi wa WhatApp, wanda ya ke da farin jini sosai tsakanin iyalai da abokan aiki da kuma na arziki da ke cikin kasar da kuma kasashen waje.

Kashi casain da uku cikin dari na masu amfani da shafin internet na amfani da shafin WhatApp a cewar kamfanin Techcrunch, saboda matasa da dama da kuma marasa galihu da ke kasar sun dogara kan sakonin da ake turawa kyauta a shafin da kuma ta wayar tarho.