Kotu ta soke zaben gwamnan Akwa Ibom

Hakkin mallakar hoto Akwa Ibom Govt Facebook
Image caption Udom zai iya daukaka kara

Kotun daukaka kara a Abuja ta soke zaben gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP.

Kotun ta ce an tafka magudin zabe a lokacin da aka ayyana Udom a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a ranar 11 ga watan Afrilun 2015.

Alkalan kotun karkashin jagorancin, mai shari'a Uwani Abba Aji sun umurci hukumar zaben Nigeria ta gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 90 a kananan hukumomi 31 na jihar.

Dan takarar jam'iyyar APC, Umana O Umana ne ya shigar da kara kotu a kan cewar an yi aringizon kuri'u a zaben da aka bai wa PDP nasara a watan Afrilu.

Mr Emmanuel na jam'iyyar PDP na da damar kalubalantar hukuncin a kotun koli.