Biafra: An kashe mutane biyar

Hakkin mallakar hoto Nnamdi Twitter
Image caption Ana zargin Kanu da harzuka mutane domin su yi wa gwamnati tawaye.

Rahotanni daga Najeriya sun ce an kashe biyar daga cikin mutanen da ke goyon bayan Nnamdi Kanu, mutumin da ke son kafa kasar Biafra a birnin Onitsha.

'Yan sanda sun tabbatar da harbin mutane da ke zanga-zanga, sai dai sun ce uku daga cikinsu ne suka mutu.

Sun zargi masu zanga-zangar da ji wa wani soja rauni da kuma lalata bindigarsa.

Lamarin ya auku ne bayan wata kotu da ke Abuja ta bayar da umarni a saki Mista Kanu ranar Alhamis, lamarin da ya sa masu goyon bayansa suka rika murna.

Ana zargin Mista Kanu da watsa labaran da ke harzuka mutane a gidan rediyonsa na Biafra.