Burundi ta maida Martani

Gwamnatin Burundi ta mayar da martani cikin fushi dangane da kudirin Kungiyar tarayyar Afirka na kai wa kasar dauki ta hanyar tura sojoji dubu biyar, wadanda za su yi aikin wanzar da zaman lafiya da kare farar-hula.

Kakakin gwamnatin, Philippe Nzobonariba ya shaida wa BBC cewa kasarsa za ta kalli wannan mataki na kungiyar tarayyar Afirka tamkar kai wa Burundi hari ne, idan aka tura sojojin ba tare da amincewarta ba.

Kwamitin sulhu na kungiyar tarayyar Afirka ne ya amince da wannan kudirin, amma zai bukaci goyon bayan Majalisar dinkin Duniya kafin ya zartar da kudirin.

Akalla mutum 400 ne suka halaka a Burundi, daga watan Afrilun da ya wuce sakamakon rikicin da ya biyon bayan yunkurin shugaban kasar, Pierre Nkurunziza na yin ta-zarce.