An ci tarar asibitin kula da masu cutar HIV Fam 250

Hakkin mallakar hoto PA

An ci tarar wani asibiti Fam 250 da ya bayana sunnayen wasu da ke dauke da cutar dake karya garkuwa jiki cikin kuskure.

Kuskuren ya faru ne ta wani sakon e-mail da aka aika kuma masu dauke da kwayar cutar suka samu.

Wannan abun ne dai ya janyowa asibitin tarar Fam 250 daga hukumar da ke sa ido ta kasar Ingila game da bayanan da ke kumshe a cikin sakonni .

Wata kungiya da ake kira Bloomsbury Patients Network da ke tallafawa masu dauke da wannan cuta ta HIV ta samu labarin.

A shekarar 2014 sau biyu ,sakon ma'aikatan asibitin da ya kai 200 , cikin kuskure ya shiga e-mail din wadanda suke dauke da kwayar tutar ta HIV.

Na farko a watan Favararun shekara na biyu a watan Mayu.

Ma'aikatar yadda labarai ta sanar da cewa an yi tarar ne ta yadda ba za ta jijiga asibitin ba ta fanin kudi.