El-Zakzaky: An yi zanga-zanga a Tehran

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Shi'a na so a saki El-Zakzaky

Dubban 'yan Shi'a a Iran sun yi zanga-zanga a Tehran domin nuna adawa da kashe wasu 'yan Shi'a a Nigeria.

Masu zanga-zangar sun kuma bukaci a sako shugaban 'yan Shi'a na Nigeria, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

A karshen mako ne an samu rikici tsakanin 'yan Shi'a da sojoji, lamarin da ya janyo mutuwar 'yan shi'a sama da 200.

A yanzu haka dai El-Zakzaky na hannun jami'an tsaro sakamakon hatsaniyar da aka samu.

Tuni shugaban Iran, Hassan Rouhani ya kira shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari a kan batun inda ya bukaci a daina gallazawa 'yan Shi'a.