Kotu ta bayar da belin Sambo Dasuki

Dasuki na cikin tsaka mai wuya
Bayanan hoto,

Dasuki na cikin tsaka mai wuya

Wata babbar kotun Abuja ta bayar da belin Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa tsohon shugaban kasar Najeriya shawara kan tsaro.

Kazalika kotun ta bayar da belin sauran mutane hudu da ake zarginsu tare da Dasuki bisa laifuka 19 da ke da alaka da halatta kudin haram da zamba cikin aminci.

Sauran mutanen da ake zargi da laifukan su ne: tsohon daraktan kudi a ofishin Sambo Dasuki, Shuaibu Salisu da tsohon Darakta na kamfanin mai na NNPC, Aminu Baba Kusa da kamfanin Acacia Holdings Limited da kuma asibitin Reliance Reference.

Mai shari'a Husseini Baba Yusuf ne ya bayar da belinsu a kan Naira miliyan 250 kan kowanne su, sannan kowannen su ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa - kuma dole mutanen su kasance tsofaffin manyan ma'aikatan gwamnati masu mukaman darakta.

Sannan kuma an bukaci mutanen su mika fasfo dinsu ga babban akawu na kotun tarayya kuma sai sun gaya wa kotun kafin su yi balaguro zuwa wajen Abuja.