An saki wasu 'yan Shi'a a Kaduna

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu ana ci gaba da tsare El-Zakzaky.

Jami'an tsaro a jihar Kaduna da ke Najeriya sun ce sun saki wasu daga cikin 'yan kungiyar Islamic Movement, watau 'yan Shi'a wadanda aka kama yayin rikicin da 'yan kungiyar suka yi da sojoji a Zaria.

A ranar Asabar din da ta wuce ne dai sojojin suka kama 'yan Shi'a da dama, kaana suka mika su ga 'yan sanda bayan sun yi arangama da su, sakamakon zargin da sojoji suka yi musu na yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa, Janar Tukur Barutai.

Hukumomi sun ce an saki mata da yara kanana masu yawa ba tare da wani sharadi ba.

Har yanzu dai ana ci gaba da tsare shugaban kungiyar ta Islamic Movement, Sheikh Ibrahim el-Zakzaky.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alkawarin kafa kwamitin da zai binciki lamarin.