Kasashen Duniya sun Daidaita kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Bakin manyan kasashen duniya da ke taro a New York ya zo daya wajen amincewa da wani shirin wanzar da zaman lafiya a kasar Syria, amma taron bai fayyace makomar shugaba Bashar Al Assad ba.

Wata mai ba wa shugaba Assad shawara, Bouthaina Sha'aban ta ce kasashen duniyar sun yi daidai, saboda ba ruwan biri da gada

Ta ce yin haka shiga sharo ne ba shanu, karan-tsaye ne ga gwamnatin syria da al'umarta. Ban san a ina ake haka ba, a ce wata kasa ta bude baki tana maganar 'yancin shugaban wata kasa na ya ci gaba da mulki ko ya sauka.

Shirin, wanda Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya amince da shi ya bukaci a dakatar da bude-wuta a baki dayan Syria.

Kazalika shirin ya fitar da jadawalin gudanar da zabe a kasar, wanda Majalisar dinkin duniya za sa-ido a cikin wata 18, yana jaddada cewa za a ba wa al'umar Syria damar yanke shawara a kan makomar kasarsu.

Haka kuma shirin ya bayyana cewa ba za a shigar da kungiyoyin 'yan tawayen da aka sanya a rukunin 'yan ta'adda a cikin tattaunawar sulhun ba, wato kungiyoyi irin su IS da Al Nusra Front, saboda haka za a ci gaba da yakar su.