An kashe mutane 75 a Habasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kabilar Oromo a Habasha

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human rights Watch ta ce tun bayan fara zanga-zanga a watan daya gabata a kan fadada Addis Ababa babban birnin kasar Habasha 'yan sanda da sojoji sun kashe mutane saba'in da biyar.

Gwamnatin kasar ta ce mutane biyar kawai aka kashe da ga cikin masu zanga-zangar 'yan kabilar Oromo wadanda sune mafi yawa a kasar.

'Yan kabilar ta Oromo sun ce shirin da gwamnati ta ke na mayar da dajin da ke yankinsu fili, zai sa manoma da yawa su rasa gonakinsu.

Gwamnatin kasar dai na zargin masu zanga-zangar da aikata ta'adancin a kan fararen hula.

Kungiyar ta Human rights watch ta ce rashin daukar kwakkwaran mataki daga gwamnatin kasar zai iya janyo asarar rayuka da yawa.