Jiragen Amurka sun kashe sojojin Iraqi tara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ash Carter ya mika sakon ta'aziyyarsa ga mahukuntan Iraqi

Sakataren harkokin tsaron Amurka, Ash Carter ya mika sakon ta'aziyyarsa ga mahukunta a Iraqi bisa mutuwar sojojin su tara da suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare ta sama da Amurka ta kai.

Sojojin Amurka sun ce hare-haren da suka kai a kusa da birnin Falluja, an kai shi ne bayan bukatar taimakon da Iraki ta nema domin a taimaka mata da kai hare-hare ta sama dan sojojinsu su samu galaba a kan 'yan kungiyar IS.

Mr Carter ya ce an samu kuskure wajen kai harin ta sama wanda ya taba dukkan bangarorin biyu.

Mr Carter na wannan maganar ne lokacin da ya kai ziyara katafaren jirgin ruwan yakin dakarun Amurka da ke yankin Gulf.

Kazalika ya kai ziyara wajen da jiragen saman Faransa suke wadanda ake amfani da su wajen kai hare-hare ta sama a kan kungiyar IS da ke Iraki da Syria.