Shugaba Kagame zai yi 'tazarce'

Hakkin mallakar hoto AP

Sakamakon wucin gadi na zaben raba gardama a Rwanda dangen da sauya kundin tsarin mulkin kasar ya nuna shugaba Kagame zai iya zarcewa akan mulki.

Hukumar zaben kasar ta ce, kashi casa'in da takwas na wadanda suka jefa kuri'a sun yi na'am da ci gaba da mulkin Paul Kagame.

Shugaba Kagame ya kasance mai karfin gaske a fagen siyasar Rwanda tun bayan kisan kare dangi na shekarar 1994.

Amurka da tarayyar Turai sun yi Allah wadai da yunkurin na sauya kundin tsarin mulkin da zai baiwa shugaba Kagame damar yi wa'adin mulki na uku.