An kai hari Somaliya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani abu ya fashe a Mogadishu

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon wani bam da ya tashi a cikin wata mota a tsakiyar Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Ganau sun ce wasu 'yan bindiga ne suka da na bam din a motar, kana su ka kuma bude wuta a babbar hanyar Maka al-Mukarama.

Wasu da dama kuma sun jikkata.

Har yanzu dai ba san wanda ke da hannu a fashewar abin ba.

A baya dai mayakan kungiyar al-shabaab sun kai hare-hare da dama a kan hanyar a makonnin da suka gabata inda suka kashe wata mace 'yar jarida da kuma wani babban jami'in a hukumar leken asirin kasar.