Niger: `Yan Jarida na zargin mahukunta da zagon-kasa

Shugaban Niger Muhammadu Isufu Hakkin mallakar hoto FAROUK BATICHE AFP

A jamhuriyar Nijar 'yan jarida na kuka, tare da zargin cewa hukumomin kasar na kama galibin wadanda suke zantawa da su, musamman bangaren 'yan adawa, lamarin da suka ce tamkar zagon-kasa ne ga aikin jarida a kasar.

Kukan na 'yan jarida na baya- bayan nan dai na zuwa ne bayan da 'yan sanda suka kama Doudou Rahama na jam'iyyar adawa ta CDS Rahama.

'yan jaridar na zargin an kama Doudou Rahama ne saboda hirar da ya yi da BBC ranar Juma'ar da ta gabata, inda ya karyata zargin da shugaban kasar Muhammadu Isufu ya yi cewar an yi yunkurin yi masa juyin mulki.

Kawo yanzu dai bangaren gwamnatin Niger bai mai da martani dangane da wannan zargin ba.