Ana ci gaba da wahalar Mai a Najeriya

Layin Mai a Najeriya
Image caption Watanni biyu kenan ana fama da matsalar karancin Mai a kasar.

A Najeriya matsalar karancin man Fetur na ci gaba da zama babban kalubale da ke damun al'umar kasar.

Yawancin jihohin kasar na cikin matsalar rashin man Fetur din, inda daruruwan motoci kan dasa dogon layi a gidajen Mai.

Wasu daga cikin gidajen Mai dai na garkame ne saboda rashin man, ya yin da a wasu garuruwan jihar Adamawa Lita daya ta mai ta kai Naira dari da tamanin a wasu gidajen Mai.

A birnin Tarayya Abuja kuwa, layin mai har Zobe ya ke yi, inda wasu masu ababen hawa kan kwana su Hantse a layin mai ba tare da an zo kan su ba. Kusan watanni biyu kenan aka shafe ana fama da matsalar karancin man Fetur a Najeriya.

Ko a watan da ya gabata a rahoton da Bankin Duniya ya fitar kan tattalin arzikin kasar ya shawarci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da a cire tallafin Mai, a cewar bankin dawainiyar Tallafin Man ta fi alfanunsa yawa.