Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kunshin da aka samu a Jirgin Faransa ba shi da lahani

Shugaban Kamfanin sufurin jiragen saman Faransa, Frederic Gagey, ya ce kunshin da aka gano a wani jirgin saman kamfanin da aka karkatar zuwa birnin Mombasa na Kenya mai tashar jiragen ruwa, wanda kuma aka yi zargin bam ne, ba shi da wani abu na lahani.

Ya sheda wa manema labarai cewar bai da karfin fashewa ko kuma lalata jirgin sama, to amma wani hadi ne na katako da takardu da kuma wani makunni.

Jirgin samfafarin Boeing 777 na kan hanyarsa ne ta zuwa Mauritius zuwa Paris, a lokacin da matukin jirgin ya nemi yin saukar gaggawa.

An gano na'urar ce a ban dakin jirgin.

A halin yanzu filin jirgin Mombasa ya koma ayyukansa sannan ana dora fasinjoji a kan wasu jirgen masu zuwa Paris.