Sababbin Jama'iyu na neman iko a zaben Spain

Mai zabe a Spain Hakkin mallakar hoto Getty

Masu zabe a Spain na tafiya zabe a wani babban zaben da sababbin jama'iyun siyasa ke kalubalantar jama'iyu 2 da aka saba da su.

An yi hasashen cewar jama'iyar masu ra'ayin yan mazan jiya ta Popular ta Pirayim Minista Mariano Rajoy, wadda ta lashe zabe tare da gagarumin rinjaye shekaru 4 da suka wuce, za ta rasa rinjayenta, to amma za ta ci gaba da zama babbar jama'iya a gaban yan gurguzu.

Sai dai kuma ana sa ran sababbin jama'iyun da aka kafa jama'iyar Podemos mai kin jinin tsuke bakin aljihu da kuma jama'iyar masu sassaucin ra'ayi ta Liberal Citizens za su samu nasara mai dama a zaben.

Kafin zaben dai kashi 40 cikin dari na masu kada kuri'a sunce ba su yanke hukunci a kan wanda za su zaba ba.

Masu lura da al'amura sunce sakamakon zai iya haddasa wani lokaci na rashin tabbas ko kuma wata sabuwar siyasar hadin kai.