Kungiyoyi masu akidar IS na karuwa

Mayakan IS Hakkin mallakar hoto APTN
Image caption Barazanar kungiyar IS na ci gaba da zama kalubalen tsaro a wasu kasashe.

Wani sabon nazari ya bayyana cewar kasashen yammacin duniya na yin kasadar gazawar manufa muddun suka mayar da hankali kawai a kan murkushe kungiyar IS da karfin soji.

Nazarin ya ce dakarun yan tawaye akalla 15 ne a Syria suke da akidar jihadi makamanciya kwarai da gaske, kuma za su iya cike duk wani gibin da murkushe kungiyar IS zai haifar.

Rahoton wanda cibiyar nazarin addini da yanayin siyasa --- wadda keda alaka da tsohon Pirayim Ministan Birtaniya, Tony Blair ta fitar -- ya bayyana cewar yayin da ake mayar da hankali mai dama a kan kokarin gamawa da kungiyar IS, ana kuma yin watsi da barazanar da kungiyoyi masu ra'ayi iri daya ke yi.