Taliban ta daidaita sansanin 'yan sanda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Taliban suna ci gaba da ta'asa a Afghanistan

Wani babban jami'in 'yan sandan gundumar Sangin da ke kudancin Afghanistan, ya ce mayakan Taliban sun daidaita baki dayan shalkwatar 'yan sanda da ke yankin Helmand.

Kwamanda Muhammad Dawood ya ce 'yan sanda da sojoji sun sha damara, cikin shirin ko ta kwana.

Amma ya ce halin da ake ciki a wurin ya munana, bayan shafe kwanaki biyu ana bata kashi da mayakan na Taliban, akwai kuma gawawwakin sojoji da wadandan suka jikkata a sansanin su, ya yin da su ke cikin matsalar karancin abinci da makaman yaki.

Dawood ya shaidawa BBC cewa idan ba a dauki matakan da suka kamata ba, nan da sa'o'i kadan 'yan Taliban za su kwace iko da sansaninsu.

A wani rahoton na daban kuma, wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan dakarun hadin gwiwa na Amurka da Afghanistan a kusa da sansanin Sojin sama da ke Bagram inda ya hallaka sojoji biyar.