An dage dokar hana 'yan luwadi bayar da agaji

Hakkin mallakar hoto ISNA
Image caption Masu bayar da agajin jini

Gwamnatin Amurka ta dage dokar hana masu luwadi bayar da agajin jini, wacce aka kafa tun a shekarar 1983 lokacin da cutar AIDS, ko Sida ta bullo.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka ta ce za a bar maza masu luwadi su rika bayar da agajin jini, idan dai ba su yi luwadin ba a cikin shekara daya.

Sai dai duk da haka, wasu masu rajin kare hakkin 'yan luwadi a kasar sun ce duk da sassaucin, dokar tana nuna wariya.

Sun ce idan aka yi amfani da hanyoyin gwajin cutar Sida na zamani, zai rage jinkirin da ake samu wajen bayar da agajin jinin.

Hukumar kula da ingancin magungunan ta Amurka ta ce har yanzu dokar hana masu sana'ar karuwanci bayar da agajin jini tana nan.