Dabarar kai mutane a baro ta Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Screengrab
Image caption Mayakan Boko Haram sun hallaka dubban mutane

Rundunar tsaron Nigeria ta yi zargin cewar kungiyar Boko Haram ta bullo da wata sabuwar hanya ta yaudara domin hallaka mutane.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Birgediya Janar Rabe Abubakar ya fitar, ta ce daga cikin yaudarar da 'yan Boko Haram ke yi, har da kwanciya a kasa mutum ya yi ta kuka yana kururuwa kamar ba shi da lafiya, idan mutane sun taru don taimaka masa, sai ya tayar da bam.

Rundunar ta ce dan kunar bakin wake a Damaturu, ya yi amfani da wannan yaudarar domin hallaka jama'a.

Haka kuma 'yan kunar bakin wake na amfani da rabon kudi domin jan ra'ayin mutane sannan su tayar da bam kamar yadda suka yi a Yola.

Rundunar tsaron ta shawarci jama'a su yi hattara domin kaucewa fadawa cikin irin wannan tarkon.