An bayar da sammacin kama Campaore

Hakkin mallakar hoto
Image caption Campaore ya shafe shekaru 27 a kan mulkin Burkina Faso

Hukumomi a Burkina Faso sun bada sammaci na kasa da kasa, domin kama tsohon shugaban kasar, Blaise Compaore.

A shekarar da ta wuce aka hambarar da Mr Compaore daga mulki.

Mr Compaore wanda a yanzu yake zaman gudun hijira a Ivory Coast, ana zarginsa da hannu wajen kashe tsohon shugaban kasar, Thomas Sankara a shekarar 1987.

Gwamnatin rikon kwayar Burkina Faso ce ta bada umurnin a sake duba abin da ya janyo mutuwar Sankara a lokacin ana kokawar mulki a kasar.

Kuma tuni ana kama wasu manyan sojoji inda aka soma tuhumarsu kan batun mutuwar Sankara

A cikin watan Mayun bana ne aka tono gawar Mr Sankara domin sake binciken abin da ya janyo rasuwarsa.