An yi kutse a madatsar ruwa a Amurka

Masu kutse 'yan kasar Iran sun kutsa cikin kwamfutocin kasar Amurka da ke kula da wata madatsar ruwa kusa da birnin New York.

Jaridar Wall Street Journal wacce ta ambato hakan, ta ce harin wanda aka kai a shekarar 2013, bai yi wata illa ba, sai dai an saci bayanai game da yadda ake magance ambaliyar ruwa daga madatsar.

Masu kutse daga wasu kasashe sun sha yin kuste a ma'aikatun Amurka.

A cikin shekaru 10 da suka wuce, kusan sau goma sha biyu masu kutse na samun nasarar harin wasu ma'aikatu a Amurka.

Cikakkun bayanai game da madatsar ruwan ta Bowman Avenue a Rye, sun nuna yadda wani bincike ke alakanta asalin masu harin da Iran, sannan aka ankarar da Amurka da ta dauki mataki.

Gungun masu kutsen da suka saci bayanai a madatsar ruwan da Bowman Avenue, an taba samun shi da kaddamar da kutse a wasu cibiyoyin hada-hadar kudade na Amurka.

Masu kutsen sun kuma kai hari da dama a wasu kamfanonin samar da lantarki na Amurka, sai dai basu taba katse lantarkin ba.

Masu bincike suna ganin masu kutsen za su iya amfani da bayanan da suka sata a ma'aikatun samar da lantarkin wurin bata dangartakar diplomasiyya tsakanin Amurka da Iran.