Afrika na fama da barazanar 'yan Jihadi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'an tsaron Najeriya dai sun samu nasarori a yaki da Boko Haram, inda suka tarwatsa sansanonin su da dama.

Binciken da aka yi na kwana-kwanan nan ya nuna cewa, Boko Haram ce ta fi munanan ayyuka cikin kungiyoyin 'yan ta'adda, inda har ta sha gaban kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulinci, watau IS barazana ga zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Rahotannin da ake samu na yau da kullum daga rundunar sojin Najeriya na nuna cewa dakarun na ci gaba da tarwatsa sansanonin kungiyar na Boko Haram.

Sojojin na tsare da wadanda ake zargi su ne jagororin kungiyar, yayin da ake 'yanta wadanda kungiyar ta sace kuma ake nuna hotunan ayyukan da suke gudanarwa.

Ana samun galaba a yaki da mayakan kungiyar, ta hanyar dakile kashe-kashen da suke aiwatarwa da kuma hana su iko da wasu garuruwa, ganin cewar a daidai wannan lokacin a bara Boko Haram ke iko da yawancin garuruwan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Duk da haka dai kungiyar ta Boko Haram ba ta karaya ba, kuma ta kai hare-haren bama-bamai da farmaki kan fararen hulan da ke yankin jifa-jifa.

Jami'ai a Najeriya dai suna mamakin yadda kungiyar ke samun makamai kuma suke ci gaba da kaddamar da munanan hare-hare har wa yanzu.

Hukumar bayar da agajin gaggawa watau BIR ta kasar Kamaru da ke ketare ma, ta fuskanci babban kalubale a yakin da ake yi da Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Buhari dai ya amince da kara wa sojojin wa'adi domin ganin sun kawo karshen Boko Haram.

Bai kamata Najeriya ta yi watsi da barazanar da 'ya'yan kungiyar ke yi mata ba, da kuma irin tsarin yadda suke kai hare-hare.

Ganin yadda hare-haren na su ke ta'azzar, ya sa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince cewa wa'adin da ya sanya wa sojojin domin kawo karshen yaki da 'yan ta'addar a karshen bana ba zai yiwu ba.

A wani jawabi da shugaban ya yi, ya ce "Wa'adin da aka sanya ya zama kamar wani jagora ne gare su, kuma idan kasashen da ke yaki da kungiyar suka bayar da shawarar a yi garambawul a kan batun, gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa wurin amincewa da hakan ba, musamman ganin cewa an yi yaki da kungiyar da suka yadu a wasu wuraren."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mokhtar Belmokhtar wanda ke jagorantar kungiyar al-Mourabitoun.

'Hadin gwiwa'

Kasashen tafkin Chadi da ke makwabtaka da Najeriya dai suma na gwagwamaya ganin sun dakile kungiyoyin 'yan ta'adda da ke tasowa.

Yawancin kasashen da ke yankin sahel da ke arewacin nahiyar ta Afrika ne matattarar 'yan ta'adda da dama, da kuma ke samun mafaka a wuraren.

Bai kamata kasashen Afrika da magoya bayan gwamnatocin su yi kuskuren tunanin talauci ne kadai ke janyo ayyukan ta'addanci ba, duk da cewar yana daya daga cikin dalilan, amma kuma kar su yi wa kaifin akida rikon-sakainar-kashi.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Al-Shabab dai ta sha fuskantar tirjiya a tsakanin mambobin ta.

Alamu daga kasashen da suka ci gaba dai sun nuna cewa, ba al'ummar da ke fuskantar wariya ko talauci ne kadai ke shiga kungiyoyin 'yan ta'adda kadai ba, kuma ganin yadda abubuwa suke ba yanzu ta'addanci zai bar Afrika ba.