Musulmai sun kare Kiristoci a Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan al-Shabab sun addabi al'ummar Kenya da Somalia

Wasu Musulmai da ke tafiya a cikin motar haya da mayakan Al-Shabab suka tare a Kenya, sun kare fasinjoji Kiristoci da ke tare da su a cikin motar.

Shaidu sun ce Musulman sun ki raba tsakaninsu da Kiristoci, a lokacin da 'yan ta'adda suka bukaci a ware tsakanin mabiya addinan biyu.

Mutane biyu sun hallaka sakamakon lamarin, a lokacin da 'yan al-Shabab suka tare motar wacce ta taso daga Nairobi babban birnin kasar zuwa garin Mandera da ke arewacin Kenya.

A cikin watan Afrilu 'yan al-Shabab sun hallaka dalibai 148 a jami'ar Garissa, inda suka ware Kiristoci a makarantar suka kashe su, sannan suka kyale Musulmai.

A cikin watan Nuwamba ma, mayakan kungiyar sun hallaka mutane 28 wadanda ke tafiya a cikin motar haya a kasar ta Kenya.