Taliban ta kwace lardin Helmand

Image caption Sanqin da ke laradin Hemand na da matukar muhimmanci ga dakarun taliban da kuma gwamantin Afghanistan

Kungiyar Taliban ta ce ta karbe iko da wata babbar gunduma a lardin Helmand da ke kudancin Afghanistan.

Kungiyar ta Taliban ta shaidawa BBC cewa yanzu mayakanta ne ke rike da iko da tsakiyar garin Sangin.

Mayakan kungiyar sun kuma yi wa shedkwatar 'yan sanda, da wasu gine ginen gwamnati a gundumar kawanya na wasu kwanaki.

Yayin da gwamnan Helmand Mirza Khan Rahimi ya ke cewa gwamnati ce ke rike da wuraren, mataimakinsa ya ce an kwace garin Sangin.

'Yan Taliban sun ce su ne ke da iko da yawancin garin, ciki har da shalkwatar mulki wadda aka gudu aka bari.

Tun da farko, kungiyar ta Taliban din ta ce ta kaddamar da hari a wani sansanin sojin sama a wajen babban birnin Afghanistan, Kabul, inda wani dan kunar bakin wake ya halaka sojojin Amurka shida

Harin yana daya daga cikin hari mafi muni akan sojojin kasashen waje a Afghanistan a wannan shekara. Duk da harin wanda yake daya daga cikin mafi muni a 'yan watannin nan, fadar shugaban Amurka ta White House ta ce ta dukufa wajen taimakawa gwamnati da mutanen Afghanistan.

An kai wasu karin sojojin 12,000 na kasashen waje a wani shiri da kungiyar kawancen tsaro na NATO ke jagoranta wanda ke kokarin karfafar tsaron dakarun tsaron Afghanistan.

Yakin da a ke fafatawa kan Sangin ya zo kimanin shekara guda da kawo karshen yakin da Biritaniya ke yi a Afghanistan inda aka kashe a kalla sojoji 450.