"Boko Haram ta hana yara miliyan daya zuwa makaranta"

Image caption Kadan daga cikin yaran da aka kubuto a hannun 'yan Boko Haram na samun kulawa a sansanin 'yan gudun hijira

Wani rahoto da Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya fitar ya ce sama da yara 'yan makaranta miliyan daya da rikicin Boko Haram ya ritsa da su arewa maso gabashin Najeriya ba sa zuwa makaranta.

UNICEF ya ce wannan adadi kari ne a kan kimanin yara miliyan 11 wadanda ba sa zuwa makaranta a Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar kafin faruwar rikice-rikicen kungiyar Boko Haram.

A tsakanin kasashen Kamaru da Najeriya da Chad da Jamhuriyar Nijar an rufe makarantu fiye da 2000 a shekara guda sakamakon fadace-fadacen, yayin da aka lalata darururuwan makarantu, sannan aka kona wasu.

A arewacin Kamaru mai nisa makaranta daya ce kawai aka bude a wannan shekarar a cikin makarantu 135 da aka rufe a shekara ta 2014.

A cewar Michel Fontaine, shugaban UNICEF na yankin tsakiya da kuma yammacin Afirka, asusun ya taimakawa yara kimanin 170,000 komawa makaranta a jihohi uku da rikicin Boko Haram ya yi sauki, sai dai yawancin azuzuwan wadannan makarantu na fama da cinkoso.