Ana gwabza fada a kudancin Afghanistan

Image caption Garin Sangin na da mahimmanci ga bangarorin biyu

Ana ci gaba da gwabza fada a garin Sangin da ke kudancin Afghanistan, a daidai lokacin da Sojoji da 'yan sanda ke luguden wuta a kan mayan Taliban.

'Yan Taliban na kokarin karbe iko da garin da kuma gundumomin da ke kewaye da shi.

Manjo Richard Streatfield tsohon sojan Biritaniya ne da ya yi yaki da 'yan Taliban a shekarar 2009, ya shaida wa BBC cewa "idan mayakan su ka yi nasarar karbe iko da wurin, za su samu karin kudaden shiga".

A cewarsa wurin ya na da albarkar noman ganyen Opium da ake hada miyagun kwayoyi da shi.

Ya ce masu tada kayar baya na Taliban su na samun kudaden shiga da suke amfani da su wajen sayan makamai.

Gundumar Sangin na daga cikin garuruwan da suka fada hannun 'yan Taliban a shekarar 1992, daga nan ne suka samu damar mamaye kasar baki daya.