'Kwayar cutar Bakteriyar da ba ta jin magani'

Hakkin mallakar hoto thinkstock

An gano kwayar cutar Bakteriyar da ta fi karfin maganin Colistin, wanda ya fi kowanne maganin cututtuka irin na Bakteriya a kasar Turai.

Jami'ai dai sun ce baya barazana ga lafiyar dan adam, amma ana dai kara gudanar da bincike.

Masana kimiyya sun yi gargadin cewa duniyar za ta shiga wani hali na ha'ula'i, inda magungunan da ke maganin kwayar cutar Bakteriya za su gaza yin aiki makamancin, lamarin da ya afku a kasar China a watan da ya gabata.

Yanzu dai bincike ya gano ire-iren wadannan kwayoyin cutar Bakteriyar da basu jin magani a gonaki uku, da kuma gwajin jinin mutane da aka gudanar.

Likitoci na amfani da kwayar Colistin ne idan wasu magungunan sun gaza, hakan kuma yasa ya ke da muhimmanci sosai.

A wani hasashe da likitocin suka yi, sun yi zaton suna da shekaru uku cur kafin Colistin ya rage kaifi daga kasashen China zuwa Turai, duk da cewar tun farko dama hukumomin lafiyar mutane da dabbobi sun fara gwajin karfin sa.

Hukumar kula da lafiyar Ingila dai ta gudanar da gwaje-gwajen magunguna kan kwayoyin cutar Bakteriya guda 24,000, kuma tana da lissafin bullowar cutar a shekarun 2012 da 2015, inda aka gano guda 15 cikin su ne suka fi karfin kwayar Colistin, cikin su har da kwayoyin cutar Salmonella da E.Coli.

Wannan bincike ba zai zo da mamaki ba, ganin yadda aka samu makamancin hakan a wasu yankunan Turai da Asiya da Afrika.

Binciken nan dai zai sa a shiga fargabar barazanar da tirjiyar da kwayar cutar ta Bakteriya ke yi, wacce ake ganin za ta mayar da duk wani ci gaba da Likitoci suka samu baya.

An dai san amfani da kawayoyin rage cuta fiye da kima da kasar China ta yi a sashen noma ya janyo raguwar karfin maganin.

Coilin Nunan, wata ma'aikaciyar kungiyar da ke fafutukar ganin an daukaka kaifin magungunan da ke yaki da kwayoyin cuta, ta ce "Muna bukatar gwamnati da hukumar tarayyar Turai da kuma sauran kungiyoyin da ke sa ido, kamar sashen da ke kula da dabbobi su kai daukin gaggawa".