Muhimman abubuwa kan kasafin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin kasar na shekara 2016 ga 'yan majalisar dokokin kasar.

Kasafin, na fiye da Naira Tiriliyan 6, ya haura na bana da ke karewa da Tiriliyan daya da rabi duk kuwa da faduwar farashin man fetur a duniya, abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.

Buhari ya ce kasafin, wanda shi ne na farko na gwamnatinsa, zai mayar da hankali ne wajen zaburar da tattalin arzikin kasar, da kawo ci gaba a kowane fannin rayuwa da kuma tabbatar da walwalar 'yan kasar.

 • ADADIN KASAFIN KUDIN : Naira Tiriliyan 6.08
 • MANYAN AYYUKA : Naira Tiriliyan 1.8
 • AYYUKAN YAU DA KULLUM : Naira Tiriliyan 2.35
 • ILIMI : Naira biliyan 369.6
 • AYYUKA, MAKAMASHI DA GIDAJE : Naira biliyan 433.4
 • AYYUKA NA MUSAMMAN: Naira biliyan 200
 • TSARO : Naira biliyan 294.5
 • LAFIYA : Naira biliyan 221.7
 • HARKOKIN CIKIN GIDA : Naira biliyan 53.1
 • SUFURI : Naira biliyan 202
 • BIYAN BASHI : Naira biliyan 1.36
 • GANGAR MAI : Dala 38
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya ce zai yaki cin hanci da rashawa