Ghana ta tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Ghana John Manama a lokacin da ya ke shan rantsuwar kama aiki

Shugaba John Mahama na Ghana ya hana ministoti da manyan jami'an gwamnatinsa tafiye tafiye da tikitin jiragen sama masu tsada.

Shugaban ya yi hakan ne da nufin rage barnar kudade da kuma taka wa manyan jami'an gwamnatin birki wajen kashe kudade ba bisa ka'ida ba.

Masu nazarin al'amura a kasar na kallon wannan mataki da cewa ya na cikin yarjeniyar da kasar ta yi da hukumar lamuni ta IMF duk da cewa gwamnatin ba ta furta haka ba.

Majalisar kasar na shirin zartar da wani kudurin doka da ta tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda ya ki ya kin bin dokar.

Jam'iyyun adawar kasar sun dade suna zargin jami'an gwamnati da facaka da kudaden gwamnati da cin hanci da rashawa a inda suke mayar da hakan taken yakin neman zabensu a babban zaben kasar da za'a gudanar a shekara mai zuwa.