"'Yan cirani sama da 1m sun shiga Turai"

Image caption Mafi munin hanyar tsallakowa na tekun da ke tsakanin arewacin Afrika da kasar Italiya.

Yawan masu gudun hijira da 'yan ciranin da suka shiga Turai a shekarar 2015 sun wuce miliyan daya.

Alkaluman da aka fitar kwanan nan sun nuna cewa wannan yawan ya rubanya yawan shigowarsu a bara sau hudu.

Hukumar kula da 'yan cirani ta duniya tana sa ido kan mutanen da ke shigoa kudancin Turai, kuma ta ce sama da kashi 80 cikin dari suna shigowa ne ta jiragen ruwa daga kasar Girka.

Kusan rabin daukacin su sun fito ne daga kasar Syria, kuma kashi daya cikin biyar, sun shiga daga kasar Afghanistan.

An kimanta mutane 3,700 ne suka rasa rayukansu a yunkurinsu na tsallaka tekun Bahar Rum, inda mafi munin tafiyar ke tsakanin yankin arewacin Afrika da kasar Italiya.

Tururuwar da mutane ke yi cikin Turai, wadanda rabon da a samu irin ta tun yakin duniya na biyu, ta tilastawa gwamnatocin kasashen Turai neman mafita ta hanyar hadin kai, amma hakan ya janyo cece-ku-cen da ke da alaka da siyasa.