Za a sa ido kan yara masu amfani da intanet

Image caption Daliban firamare

Sakatariyar ilimi a Ingila Nicky Morgan ta ce ya zamo wajibi makarantun firamere su rika sa ido sosai kan yadda dalibai ke amfani da intanet don kare su daga daukar tsattsaurar akida.

Ministoci a kasar suna nuna damuwa game da yadda masu 'tsattsaurar akidar addini ke neman cusa akidar a cikin masu karancin shekaru, ta hanyar amfani da kwamfutoci a makarantu.

Misis Morgan ta ce wasu daga ckin daliban firamare sun iya ganin wasu bayanai game da kungiyar IS.

Kungiyoyin malamai sun ce makarantu a Ingila za su yi marhabin da tsarin idan a ka musu cikakken bayani a kan shi.

Tsarin da ake neman bullo da shi, wanda yanzu aka riga aka wallafa, ya biyo bayan rahotannin da a ka samu ne kan yadda yara ko dai suka yi balaguro, ko kuma suka yi yunkurin yin balaguron zuwa Syria.

A watan Fabrairu, wasu mata 'yan makarantar Bethnal Green Academy, Shamima Begum da Amira Abase, 'yan shekaru sha biyar biyar, da kuma Kadiza Sultana 'yar shekaru 16 suka je Syria daga London.