Rasha ta kashe farar hula 200 — Amnesty

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen saman Rasha sun fara yin luguden wuta a Syria a watan Satumba.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce tana da shaidar da ke nuna cewa hare-haren da Rasha ta kai ta sama a Syria a watan Satumba sun kashe daruruwan farar hula tare da yin mummunar barna.

Kungiyar ta fitar da wani rahoto da ta hada a sakamakon hirar da ta yi da shaidu da likitoci da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam a Syria.

Amnesty ta ci gaba da cewa ta yi bincike kan hare-hare sama da 25 -- ciki har da wanda Rasha ta kai a Homs, da Hama, da Idlib, da Latakia da kuma Aleppo.

Rasha ta kai wadannan hare-haren ne a yankuna biyar a tsakanin 30 ga watan Satumba zuwa watan Nuwamba na shekara 2015.

Kungiyar Amnesty ta kara da cewa Rasha ta kai hari ne a kan gidajen jama'a da asibitoci da kasuwanni da kuma wani masallaci.

Sai dai Moscow ta dage cewa ta kai hare-haren ne a kan kungiyar IS da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai.

Rasha dai ta soma kai hari ne a kan kungiyar IS da kuma wasu kungiyoyi a bisa rokon shugaban na Syria Bashar Al Assad.