Kudan Zuman daji na neman bata a Amurka

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani sabon bincike ya nuna cewa daukacin kudan zuman daji da ke Amurka sun ragu a inda ake samun su saboda karuwar gurbatacciyar iskar gas.

Binciken, wanda aka wallafa a mujallar jami'ar kimiyya ta kasar, ya ce a tsakanin shekarar 2008 da 2013, yalwar kudan zuma ta kara raguwa da kusan kashi daya cikin hudu a Amurka, sakamakon sauyin da aka samu na noman masara saboda samar da sinadarin ethanol.

Masana kimiyya sun ce idan hakan ya ci gaba to zai tarwatsa harkar noma, kuma zai sanya manoma dogara da masu kiwon kudan zuman domin kasuwanci.