Shin zabe zai kawo karshen tarzomar Afrika ta Tsakiya?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Al'ummar Afrika Ta Tsakiya, lokacin da suke jiran isowar Paproma Francis, lokacin da ya kai ziyarar kasar a kwanan baya.

Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, inda masu zabe za su kada kuri'unsu a ranar 27 ga watan Disamba, bayan an shafe shekaru uku ana fama da tarzoma a kasar.

Gamayyar kawance ta Musulmai watau Seleka ta kwace mulki a watan Maris din shekarar 2013, daga bisani kuma wata kungiyar hadin kan Kiristoci, watau Anti Balaka ta yi juyin mulki abin da ya jefa kasar cikin tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da addini.

An samu sauyi a shugabancin kasar a watan Junairun shekarar 2014, bayan haka kuma an dage zabuka sau hudu tun daga watan Fabrairun shekarar 2015, sanadiyyar matsalolin rashin tsaro da rashin kayan aiki, duk da sa idon kungiyoyin zaman lafiya daga kasashen waje.

'Waye ke neman shugabanci?'

Image caption Tsohon firayi ministan kasar Afrika Ta Tsakiya, Martin Ziguele yana cikin na gaba-gaba a yakin neman zaben shugabancin kasar.

Tsohon firayi minista kasar Martin Ziguele, wanda masani ne kan harkar tattalin arziki, kuma ya shugabanci tsohuwar jam'iyyar da ke da rinjaye watau MLPC. Ya sha alwashin dawo da martabar jami'an tsaron kasar, da kuma hukunta duk wadanda ke da hannu a laifukan da suka danganci cin zarafi.

Sai kuma Fidele Gouandjika, wani attajiri da ke da kwarewar kan gudanar da gwamnati na shekaru da dama, kuma ya sanya wa al'ummar kasar kishin kasa ta hanyar kira gare su da su 'yanta kansu daga mulkin mallakar kasar Faransa.

Image caption Wasu sun sa hannu a wani zaben raba gardamar da aka gudanar a farkon watan Disamba, domin amincewa da sauyin kundin tsarin mulkin kasar.
Image caption An kirkiro kungiyar mayakan da ke adawa da kungiyar Balaka a shekarar 2013 saboda su dakile mamayar mayakan tawayen Seleka.

Wasu su biyu kuma cikin masu yakin neman zaben su ne 'ya'yan tsofaffin shugabannin kasar da Sylvain Patasse-Ngakoutou da kuma Jean Serge Bokassa.

Tsohuwar ministar bayar da agaji, Regina Konzi-Mongot ma tana ciki, kuma ita ce kadai macce cikin masu neman kujerar shugabancin kasar.

Kotun tsarin mulki kasar ta wanke mutane 30, kuma ta katse hanzarin wasu 14, ciki har da shugaban da aka hambarar, watau Francoise Bozize da kuma jagoran mayakan tawayen da ke adawa da Balaka, Patrice Edouard Ngaissona.

Ana yi wa duk su biyun kallon jagororin mayakan kirista da aka daura wa alhakin mummunan kashe-kashen da aka aiwatar ga al'ummar musulmin kasar.

'Shin zaben zai kawo karshen yakin?'

Ba lallai ba. Haramtawa kungiyoyin mayakan sa kai daga yin zabe zai iya janyo tarzoma nan gaba.

An kuma kiyasta mayaka a kasar za su kai miliyan 4.8.

Mayakan da ba su da wani tsayyayen shugabanci, kuma ba sa bin doka da oda.

Image caption Mayakan kungiyar musulmi na Seleka, wadanda suka kwace ikon babban birnin kasar Bangui a shekarar 2013. Wani sabon gwamnati dai ya canje su tun bayan nan.

A baya dai shugaban kungiyar ta Seleka, 'Janar' Noureddine Adam ya ce ba za a gudanar da zabe a yankinsa na arewcin kasar ba, inda yawanci mabiya addinin musulunci ne.

Bayan ganawar da ya yi da kungiyar kasashen hadin kan musulmi ta OIC, a kasar Chadi da ya yi kwanaki kalilan kafin zaben, sai ya ce zai bayar da gudunmuwa ta musamman ga zaben, kuma ya janye furucin sa na neman aware.

Image caption Jami'an tsaron Majalisar Dinkin Duiniya da na kasar Faransa na ci gaba da bayar da agajin tsaron a kasar, duk da tarzomar na ci gaba.

Ba a samu daidaito wurin zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya ba, duk da cewar akwai dakarun sojin Majalisar Dinkin Duniya da na kasar Faransa a kasar.

Ba lallai zaben kansa ya janyo wani tashin hankali ba, amma zai iya ta'azzara dangantakar da ta riga ta yi tsami tsakanin 'yan siyasa, kuma mayakan na iya amfani da wannan damar domin tayar da kayar baya.