An yi taro tsakanin Kirisitoci da Musulmai a Kano

Image caption Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ne ya kirkiro taron don kyautata dangata tsakanin mabiya addinan biyu

An gudanar da wani taron zaman lafiya tsakanin shugabannin addinin Musulunci da na Kiristanci a jihar Kano a arewacin Nigeria.

Taron wanda gwamnatin Kano ta shirya, shi ne irin sa na farko da bangarorin biyu suka tattauna kan wasu matsaloli da suke addabar mabiyan su.

A hirarsa da BBC gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce makasudin shirya taron shi ne hada kan mabiya addinan biyu domin zaman lafiya.

Sannan ya kara da cewa gwamnati za ta kafa wani kwamiti mai karfi na mabiya addinan biyu wanda zai rika ba gwamnati shawara.

Cikin wadanda suka gabatar da makala a taron sun hada da shugaban Hisbah Malam Aminu Daurawa da Rabaran Fika John sakaren kungiyar Kiristocin Najeria reshen jihar Kano