An takaita zirga-zirga a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta hana shiga da fita daga Maiduguri, ta kuma takaita zirga-zirga a cikin birnin saboda bikin Kirisimeti

An takaita zirga-zirga a Maiduguri babban birnin jihar Borno daga ranar Laraba zuwa ranar Litinin.

Rahotonin na cewa an hana shiga da fita daga birnin. An kuma hana zirga zirgar ababen hawa a wasu manyan hanyoyin da ke cikin birnin.

A hirarsa da BBC mai magana da yawun hedikwatar tsaron Najeriya, Kanar Rabe Abubakar ya ce rundunar sojin sun dauki wannan mataki ne domin kare lafiya jama'a a yayin da ake gudanar da bikin kirsimeti.