'Ba mu kashe yawan 'yan Shi'a da aka ce ba'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption El-Zakzaky na hannun jami'an tsaron Nigeria

Rundunar tsaron Nigeria ta musanta cewar ta kashe 'yan Shi'a da dama yayin arangamar da aka yi tsakaninsu a Zariya.

Hakan na zuwa ne bayan da kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce, an kashe akalla 'yan Shi'a 300 a rikicin.

Mai magana da yawun rundunar tsaron, Birgediya Janar Rabe Abubakar ya shaida wa BBC cewa "Na fadi ba ma kashe mutane, kun gane."

Abubakar ya kara da cewar "Batun adadin mutanen da aka kashe, ina tunani bai ma taso ba. Muna bin tsarin dokar kasa. Muna mutunta kundin tsarin mulki kuma muna aikinmu kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanada."

Human Rights Watch, ta ce sojojin Najeriya ba su da wata hujjar kashe 'yan Shi'a a Zaria, duk da ikirarin da suka yi cewa mabiya Shi'ar sun yi yunkurin kashe Babban Hafsan Sojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai.