Ministar sufurin Ghana ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto elvis
Image caption A shekara mai kamawa za a yi zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a Ghana.

Ministar harkokin sufurin Ghana ta yi murabus bayan an samu rahotannin cewa ma'aikatarta ta kashe kudaden da suka wuce kima kimanin dala 947,000 wajen yi wa motoci kirar bas fenti mai launin tutar kasar da kuma hotunan shugabannin kasar na baya-bayan nan.

Wani kamfani mai zaman kansa aka bai wa kwangilar yin fentin tare da zana hotunan shugabannin kasar hudu da suka gabata na baya-baya da suka hada da John Mahama mai ci a yanzu.

Jam'iyyun adawa da kungiyoyi masu yaki da cin hanci da rashawa sun nuna matukar damuwa kan irin makudan kudin da suka ce an kashe kan aikin, suka kuma tursasa fadar shugaban kasa yin bincike kan lamarin.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ma'aikatar sufurin ta ce Mrs Dzifa Attivor, ta yi murabus din ne sakamakon rikicin da ya shafi yi wa motocin bas 116 fenti.

Ghana dai na shirye-shiryen yin zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki cikin shekara mai kamawa, yayin da 'yan adawa ke ci gaba da sukar gwamnati kan almubazzaranci da kudi wajen bayar da kwangiloli.