Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Nnewi Gas

Asalin hoton, Nigerian Red Cross

Bayanan hoto,

Cibiyar sayar da Gas din da ke Nnewi inda gobarar ta auku.

Ana samun alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da suka rasu sakamakon gobara a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra.

Hukumomin 'yan sanda wadanda suka tabbatar da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske ba dangane da adadin mutanen da suka kone ba.

Hukumar agaji ta NEMA ta ce mutane biyar ne suka rasu a yayin da mutane bakwai suka samu raunuka.

NEMA ta ce gidaje shida da motoci 22 ne suka kone sakamakon gobarar.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce mutane hudu ne suka mutu yayinda wasu hudun suka jikkata.

Babban jami'in kungiyar ta Red Cross Umar Abdu Mairiga, ya shaida wa BBC cewa an debe gawawwakin zuwa wajen adana gawa, yayin da wadanda suka jikkata ke samun kulawa a asibitin koyarwa na jami'iar NNamdi Azikiwe.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne lokacin da wata motar dakon iskar gas ke sauke kayan data dauko a tashar iskar gas din, yayinda kuma ake sayarwa da wasu mutane gas din.

Mallam Idris, wani mazaunin garin Nnewi ne, ga kuma karin bayanin da ya yi wa wakilinmu Abdulsalam Ibrahim Ahmed:

Jami'an kashe gobara da mutanen gari sun shafe sa'o'i da dama kafin su kashe wutar.