An kai wa masu bikin kirsimeti hari a Isra'ila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yawan samun tashin hankali tsakanin Falasdinawa da Yahudawa a Isra'ila.

Falasdinawa sun kai hare-hare da dama a kan Yahudawa a yammacin kogin Jordan yayin da dubban masu yawan bude ido suka taru domin yin bikin kirsimeti.

A wani harin an dabawa wasu masu gadi biyu wuka a yankin Yahudawan, a wani kuma wani Bapalasdine ne ya yi kokarin kai wa sojoji hari da sukun-direba.

Hari na uku kuma wani mutum ne ya yi kokarin afkawa wasu sojoji da mota a wani wajan tsayawar sojoji.

An kashe duka Falasdinawan uku da suka kai hare-haren.

Yanzu haka an tsaurara tsaro a birnin Bethlehem yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan kirsimetin a cocin Nativity, inda aka ce a nan ne aka haifi Yesu Al-masihu.