MDD ta goyi bayan yarejejeniyar Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan kasar Libya sun yi zanga-zangar adawa da yarjejeniyar.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar da bangarorin da ke yakar juna a Libya suka cimma a makon jiya, na kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Yanzu haka dai, gwamnatoci biyu ne da basa ga maciji da juna suke a kasar ta Libya.

Kudurin da Majalisar Dinkin Duniyar ta amince da shi, ya kuma yi kira ga kasashe mambobin Majalisar da kada su rika sayen mai daga hannun kungiyar IS, wacce take cin karenta ba babbaka a wasu sassan kasar.

Jakadan Burtaniya a Majalisar Dinkin Duniyar ya ce ya kamata kasashen su yanke duk wata hulda da wata kungiya, sai dai kawai sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da za a kafa.