Australia: Wutar-daji ta lashe gidaje 100

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wutar-daji a Australia

Wata wutar-daji ta barke a jihar Victoria da ke kudancin Australia, kuma lashe sama da gidaje 100, bayan da ta hana bukukuwan kirsimeti.

Wutar ta shafi sanannun garuruwan da masu yawon-bude ke zuwa hutu, ciki har da Wye River da kuma Seperation Creek.

An dai ba da labarin cewa masu shakatawa da dama sun ranta-a-na-kare, haka su ma masu bukukuwan Kirsimeti suka watse, kowa na takai-takai.

Tun a karshen makon jiya ne gobarar ta barke, amma ta munana daga baya, sakamakon tsananin zafi da bushewar daji.