'Ba mu rufe kofar tattaunawa da Boko Haram ba'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dade ba a ji duriyar Abubakar Shekau ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kodayake sojojin kasar sun ci galaba kan mayakan Boko Haram, gwamnatinsa za ta bi kowace hanyar tattaunawa da su domin fahimtar da su su yi watsi da ayyukan tarzoma.

Shugaban ya fadi hakan ne a fadarsa yayin da yake karbar gaisuwar barka da kirsimati daga wasu shugabannin addini Kirista da sarakuna da ke yankin birnin Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan da a wata hira da BBC, Buhari ya bayyana cewar sojojin Nigeria sun karya lagon Boko Haram.

"A bayan suna rike da kananan hukumomi kusan 14, amma a yanzu kananan hukumomi biyu ko uku ne a Borno 'yan Boko Haram ke ayyukansu," in ji Buhari.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane 17,000 a yayin da wasu fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.