Japan za ta sasanta da Koriya kan bayi na lalata

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotannin daga Japan na cewa gwamnati tana shirin kafa wata gidauniyar kudi, da nufin warware doguwar takaddamar da take yi da Koriya ta Kudu game da 'yan matan kasar Koriyan da aka mayar da su bayi na lalata a lokacin yakin duniya na biyu.

'Yan matan da ake wa lakabi da "wurin rage zafi", an tilasta musu aiki a matsayin kilaki a sansanonin sojin kasar Japan lokacin yakin.

Kafofin yada labarai na Japan sun ce Firayiministan kasar Shinzo Abe, ya bai wa ministan harkokin wajen kasar umurnin ya warware takaddamar a ziyarar da zai kai Koriyan mako mai zuwa.

Tun da farko dama, Koriya ta Kudun ta ce hakurin da Japan din ta bayar ya yi kadan.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fara kyau, bayan sun amince su hanzarta tattaunawa a tsakaninsu.