Modi ya kai ziyara kasar Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption India da Pakistan na zaman doya da manja

Firayi ministan India, Narendra Modi ya isa kasar Pakistan, a ziyararsa ta farko a tun lokacin da ya hau karagar mulki.

Narendra Modi ya bayyana ziyarar ba-zatan ne a shafinsa na Twitter, yana mai cewar yana sa ran zai dan ziyarci takwaran aikinsa, Nawaz Sharif a Lahore.

Mr Modi na kan hanyarsa ta komawa India ne daga Afghanistan, a inda ya kaddamar da wani sabon ginin majalisar dokoki.

Shi ne kokari na baya-bayan nan na farfado da shawarwarin zaman lafiya tsakanin makwabtan masu makaman nukiliya.

Wakiliyar BBC ta ce ''Abu mafi fa'ida a nan shi ne yanayi da kuma lokacin wannan ziyara, ta kuma a daidai lokacin da Firai minista Nawaz Sherif ke bikin zagoyowar ranar haihuwarsa."